Ina yawan kunci
Ga zuciya zafi in baki gefa na, masoyiya
Ina yawan kunci
Ga zuciya zafi in baka gefa na, masoyi na
So yasamu guri ya shige da wuri
Jiki yana ta bari zuciya ta dau sanyi
Dukka mutum nagari bai shiga hadari
In ka rike Allah baka babu juyayi
Na kasan ce da so zana rayu a so
Inda bada gida nan ake kira jeji
Mai hakuri kara shi ka jiya
In lokacin yazo zaka sha miya
Ni na rike ka, wallah' ban sakin ka
Kai ne ka bani zuma shaikaran jiya
Mi zaya sa in yada kai? Kanka bantaba kai
Zana roka ma dukka lafiya
Aljannar duniya
So ne kin jiya
Taho mu kama shi, zamu sha miya
Dukkan dubarun so
Wallah' kin iya
Idan kikai mini laifi da magiya
Ki tattara min ki adana min
Kar ki sake domin ina da sojoji
Haba da kai ne
Za a sa ni lallai
A kanka kowa dolle za na kyale
Kyawun hali ne
Yasa kazama wane
Riga ta kirki sunanta bai zama kyalai
Ya sahabi
Haba habibi
Ana hubika
Masoyi ka nada kyaun niya
Ina yawan kunci
Ga zuciya zafi in baki gefa na, masoyiya
Ina yawan kunci
Ga zuciya zafi in baka gefa na, masoyi na